donforum


HOMEHome
musicMusic
videosVideos
gistsKanny
👉 LATEST DAILY UPDATES 👈

Sunday, March 11, 2018

[Novel] Gimbiya Nafeesat


Wasar ‘buya gimbiya keyi da Sultee, duk yanda yaso su had’u abun ya faskara don ta bar bin hanyar da tasan zata iya cin karo dashi. Ahmed da Amira kuwa soyayya sukesha abunsu, tuni Amira ta fitar da Sultee daga zuciyarta, sai fatan Allah yasa rabon Ahmed ne.
Yau ya kama tuesday, an gama had’a ma gimbiya kayakinta, jere kuwa an riga da anyi tun kamin a d’aura auren a sabon gidan da Sultee ya siya. Sultee ba abinda yakeson gani irin Nafisa amma ta’ki bari su had’u, yau dai ya ‘kudiri aniyar ko ta yaya sai ya ganta. Yamma lis mai martaba ya kira Nafisa don mata nasiha, ya fara da cewa “Mama na inaso ki sani aure da kike ganin nan ba wai ha’kuri bane zalla kamar yadda ake fad’a, yes dole a saka da ha’kuri amma dai biyayya da kuma soyayya shi ke sa zaman aure yayi tsawo, duk da nasan ba soyayya kukayi dashi kamin a d’aura muku aure ba, nasan Sultan zai kula dake kuma bazai ta’ba bari ki cutu ba, kar ki mishi rashin kunya sannan duk lokacin da ya saki abu karki kuskura kice baza kiyi ba, duk abinda zakiyi a gidan aurenki ki dinga tunatar da kanki cewa Aljannarki yana ‘kar’kashin ‘kafar Sultan”, ya d’auki lokaci yana mata nasiha wanda ba abinda gimbiya ke yi sai kuka, maganar daddy ya ratsata ‘kwarai da gaske. Baba Rabi, Ammi da mummy ma sun taru sun mata wa’azi sun kuma bata shawarwari yanda zata dauwamar da zaman lafiya a gidan aurenta, idon Nafisa yayi luhu-luhu don kukan da tasha.
Bayan anci dinner duk aka watse, Hauwa, Ukasha da Amira duk suka dunguma zuwa d’akin Nafisa, tana zaune tana ta tunani, ta amsa sallamarsu sai suka zazzauna. Hira sukeyi sosai sai dariya suke kwasa gwanin sha’awa, Sultee ya zo ‘kafarshi hud’u amma basu bar d’akin ba, tsaki yaja a zuciyarshi yace “Wad’annan akwai surutu, da ina zagin Nafisa akan tacika magana ashe dai surutun a jininsu yake tunda dukkansu sai zuba sukeyi”. Ammi da tazo wucewa taga Sultee ya fito daga hanyar d’akin Nafisa yasa ta doshi d’akin, tana zuwa tace “Ohh Allah, ‘karfe sha d’aya da rabi amma ku ko bacci baku da niyyar yi, oya tashi kowa ya wuce d’akinshi”, ta ‘karasa maganar tana nuna musu ‘kofa. Ukasha da Hauwa suka tashi ba don sunso ba suka musu sai da safe suka fita, Amira kuwa gyara kwanciya tayi, Ammi ta kalleta sannan tace “Ke baza kije kiyi baccin bane?”, Amira tace “A’a Ammi, anan zan kwana kawai”, Ammi ta ja guntun tsaki tace “Don Allah ki tashi tasamu tayi bacci, kinsan fah flight nasu 8 ne, zaki zauna ki cikata da surutu har ta rasa samun isashshen bacci”, Amira ta tura baki tace “Ni ba hanata bacci zanyi ba, tunda kin kore ni shikenan, sai da safe”. Tana fita Ammi ta matsa kusa da Nafisa tace “Kiyi bacci kinji?, kinga dare yayi”, “toh” Nafisa ta amsa mata, Ammi ta mata sai da safe sai ta fita ta ja mata ‘kofar.
Tana fitowa ta wajen verendah na flat na Nafisa ta kusa cin karo da Sultan, ja da baya yayi da sauri yana sosa ‘keya, rusunawa yayi ya gaisheta, fuska d’auke da murmushi ta amsa mishi sai tace “Tana ciki ai, ka shiga mana”. Murmushin mara gaskiya yayi ya kasa magana, ganin kunya yacika shi ne yasa Ammi yin murmushi kawai ta wuce. Shiga d’akin yayi da sallamarshi, lokacin Nafisa ta d’aura towel zata shiga wanka, da yake ta bama ‘kofa baya shiyasa bata ganshi ba shikuma komai nashi ya tsaya cak, kallonta yakeyi kaman zai cinyeta. Rufe ‘kofar toilet da tayi ne ya dawor dashi hankalinshi, da ‘kyar ya kai kanshi kan kujera ya zauna yana jiran fitowarta, ta d’an dade kad’an sannan ta fito, bata ma lura da mutum a d’akin ba, ta bud’e wardrobe tafito da night gown wanda riga ne iya guiwa, ta gama shafe-shafe shafenta da feshe feshe sai ta saka night gown d’in, har ta hau kan gado duk bata lura da Sultee da ke neman mutuwa a zaune ba yana kallonta baki bud’e. Ta hau gado sai ta d’an mi’ka hannunta don ta kashe bulb d’in d’akin ne ta ga mutum zaune ya ‘kura mata ido, ihu ta tsala tayi hanyar parlour da gudu, ganin taji tsoro yasa ya tashi da sauri ya cafkota kar aji ihun a waje, rufe mata baki yayi asanyaye yace “Shhhh, ni ne fah”, sai sannan ta d’an nitsu amma still jikinta yana rawa.
‘kwace kanta tayi daga ri’kon da ya mata, tsaki taja tace “Shine zaka wani shigo min d’aki ka zauna ba ko sallama?, wai ma yaushe ka shigo ne?”, murmushi ya mata sannan yace “Tun kamin ki shiga wanka na shigo amma baki ganni ba sai yanzu”, murgud’a mishi baki tayi tace “Amma kuma kasan ba kyau kallon jikin mace kana namiji ko?”, kasake ya tsaya yana kallonta yana kuma jin mamakin abinda ta fad’a amma dai sai ya fuske, cikin ko-in-kula yace “And so?, macen da na ganin ai matata ce, fiye da haka ma an halarta min zan iya yi ba kallo kawai ba”, bata tanka mishi ba ta juya da niyyar komawa kan gado, ri’ko hannunta yayi, cike da tsiwa ta juyo, ta bud’e baki zatayi magana kawai taji yakai bakinshi kan nata, sai tuttureshi takeyi amma shi sai ‘kara mannata a jikinshi yakeyi, da taga yana neman wuce iyaka sai ta sa mishi kuka, ido a raunane ya saketa ya juya ya fita ba tare da yayi magana ba. Kan gado ta fad’a ta fashe da kuka tana cewa “Yanzu shikenan ni duk abinda yaga daman yi dani zaiyi?, wallahi bazan yarda ba, shi kuma da yake bai da kunya har cikin d’akina a cikin gidan ubana yazo yake neman gwadamin tantirancin shi”, tsaki taja ta koma toilet tayi brush tana ta goga harshenta tana d’an hawaye. Adaren ranar Sultee ya tsokano ma kanshi tsuliyar dodo, gaba d’aya ya kasa samun nitsuwa, tsaki ya dinga ja yana da-na-sanin romancing din Nafisa da yayi don yasan hakan ne ya jefashi a halin da yake ciki, juyi ya dinga yi da ‘kyar bacci ya d’aukeshi.
Yau Wednesday ranar tafiyar Sultee da Gimbiya Nafee, tun asubah da suka tashi basu koma bacci ba, shiri akayi sosai, sunci sun ‘koshi sannan aka musu rakiya zuwa airport, ciki ko harda daddy da Ammi, mummy kam tace bazata iya zuwa ba tana a matsayin uwa, baba Rabi tayi kukan rabuwa da Nafisa sosai. A airport su daddy suka musu sallama zasu juya, da gudu taje ta ‘kan’kameshi da Amira tana kuka tace “Daddy don Allah mu tafi tare, Anty Amira kinga ai kinsaba da chan din, mutafi don Allah, bazan iya zama ni kad’ai ba”, ta ‘kara fashewa da wani kukan Amira na tayata, da ‘kyar daddy ya lallasheta yace “Yi ha’kuri mamana, kinga yanzu bamuyi shirin tafiya da ku ba amma ki bari in kin kwana biyu zamuzo dukkanmu kinji?”, girgiza kai tayi tana share hawaye “Daddy kayi al’kawari?”, asanyaye yace “Zan miki ‘karya ne?, in kin kwana biyu zamuzo mu dubaki, ai ba ke kad’ai bane achan, ga yayanki Sultan zai dinga kula da ke”. Cikin dishewar murya tace “Toh daddy, kuma…..”, announcement da akayi akan duk masu tafiya suyi boarding ne ya katse mata maganarta, daddy ya dafata yace “Yi ha’kuri kije, zamu dinga waya kullum”, kama hannunta Sultee yayi suka musu sallama, Nafisa sai waigowa takeyi tana hawaye har ta bar ganinsu, ji takeyi kaman a kunce auren ta huta tunda dai tasan ba sonshi takeyi ba. Acikin jirgi seat nashi ne ata window, asanyaye tace “Ayyah ya Sultee muyi exchanging seats kaji?”, cike da tausayinta yace “Okay ba damuwa”, sun lula a sararin samaniya, chan sai ya Sultee yace mata bari yaje toilet, yana tashi wani kyakkyawan saurayi bazai wuci 27-28 ba yazo ya zauna a inda ya tashi, sallama yayi mata ta amsa mishi, yace “sunana D…..”, katseshi tayi tace “Sorry please ni matar aure ce”, ya langa’bar da kai yace “Amma nayi rashin sa’a, wayene yamin shigan sauri haka?”, murmushi ta mishi tace “Yaya na ne shi”, ya d’anyi dariya sannan yace “Ohhh ko dai shine wanda ya tashi daga nan?”, wani murmushi ta sakeyi, zata bashi amsa kenan taji muryar Sultee cike da masifa yace “Excuse me, da matar mutum fah kake magana wanda hakan bai dace ba”, guy din ya tashi tsaye, ganin yanda Sultee ya wani had’e rai yasa yace “Sorry bro, wallahi bansan matar aure bace saida ta gayamin, I’m so sorry”, bai jira meh zaice ba ya koma seat nashi.
Sultee iya ‘kuluwa ya ‘kulu, kishi ne yake cinshi, “wai matata tana ma wani murmushi har suna hira?, meh ma ya gayamata da ta ji dad’i haka?”, baisan sanda yayi tsaki a fili ba, Nafisa ta kalleshi sai taga sam bata kyauta ba, ahankali tace “Sorry ya Sultee, naga kaman ranka ya ‘baci”, afusace ya kalleta sannan yace “Wai ma meh had’inki dashi da zaki wage baki kina dariya dashi?”, kallonshi takeyi cike da mamaki, ita dai tasan ba tayi dariya da guy din ba. Shareshi tayi, haka yayita masifarshi har ya gaji yayi shiru, ita ba abinda takeyi sai dariya ‘kasa-‘kasa, da taga ya saka earpiece ya rufe ido sai ta tsamman yayi bacci, shafa fuskarshi tayi afili tace “In yana bacci zaka ganshi kaman wani silent guy amma masifar shi yafishi tsawo”, bud’e ido yayi ya harareta, da sauri ta cire hannunta daga fuskarshi, cike da kunya ta sunkuyar da kai, tsaki yaja yace “Ni ne masifaffe ko?, wai nikam mesa kika raina ni ne?, don kina ganin ina sassauta miki ko?, wallahi zan iya ajiye aure a gefe na yi maganinki, kema kinsan ‘karamin aiki na ne”, ‘kwafa tayi ta tura mishi ‘keya tace “Ahaka zaka ‘kare, mutum kullum cikin masifa sai kace a kanshi aka saukeshi”, juyo da kanta yayi yace “Da waye kikeyi?”, taji tsoro amma sai ta dake tace “Haa, na ‘kira suna ne?, mutum nace, ko kai sunanka mutum ne?, A’uzubillah!!, na tsani masifa wallahi”, ganin in ya biye mata zasu tara ‘yan kallo yasa ya tura kanta har ta kusa gara kanta, bai ce mata komai ba yaci gaba da jin ‘kira’ar Sudais da ke tashi a earpiece nashi. Kusan awa biyu Nafisa tanaso ta mishi magana amma tana tsoro, gaba d’aya sai taji tanason tayi magana, shirun ya isheta gashi ta kasa bacci, chan sai ta d’anyi innocent face, ta matso daf da Sultee ta kwanta a kan kafad’arshi, bai tanka mata ba yaci gaba da game nashi a waya, da taga baiyi magana ba sai ta sakala hannunta ta cikinshi, yaji yarrr amma dai ya fuske, chan sai Nafisa tace “Ya Sultee ayyah muyi surutu mana, wallahi na gaji da zama shiru, duk sainaji kaman baki na zaiyi ciwo don banyi magana ba, kaji?”, dariya ya kusa ‘kubce mishi amma sai ya gintse dariyar, a zuciyarshi yace “Ohh Nafisa akwai surutu, shi ne in batayi ba bakinta zaiyi ciwo” amma a fili sai yace “Ni banason surutunkin nan, nagaji”, shiru tayi na d’an seconds sai kuma tace “Ya Sultee, meh kakeji a earpiece din ne?”, ba tare da ya kalleta ba yace “Kira’a nakeji”, tashi daga jikinshi tayi tace “Laa!!, ya Sultee ayyah tsammin ear piece d’aya nima bari naji”, ajiyar zuciya yayi sannan yace “Don Allah ki ‘kyaleni, banson takura, ina wayarki da baza kiji dashi ba?”
Fuskar tausayi tayi tace “Na manta dashi a gida, saidai in mun isa ka siyamin wani”, dariya yayi yace “Allah ya ‘kara, wazai saya miki wani?”, tayi murmushi tace “Kai mana”, Sultee yace “Lallai kam, ai kin ‘kare ri’ke waya kenan inaga don bazan saya miki wani ba”, kuka tasa mishi sosai hakan yasa ya jawota jikinshi ya fara lallashinta yace “Shhh, ni wasa nake miki, zan sayamiki kinji?”, tureshi tayi tace “Gwanda da ka gyara magana”, mi’ka mata earpiece d’aya yayi suka cigaba da jin ‘kira’ar suna d’an hira sama sama wanda rabi masifa ne.
Sun sauka Qatar lami lafiya, driver yazo ya d’aukesu suka nufi gida. Agajiye suka shiga parlour, gidan upstairs ne, parlourn ‘katon gaske ne, Nafisa ko zama batayi ba tace a gajiye “Ya Sultee ina ne d’akina, inaso naje na huta”, bai mata magana ba ya fara hawa sama, ganin haka yasa tabi bayanshi, wani d’aki ya nuna mata yace “Nan ne naki”, sai ya juya ya tafi. Da yake da dare suka iso kuma duk sunci abinci so sai kawai kowa yabi lafiyar gado.
Washegari bata tashi ba har wajen 10am, da wurwuri tashiga tayi wanka, tana ta Allah yasa Ya Sultee kar ya hauta da masifar tayi bacci dewa, doguwar riga tasaka sannan ta tsaya ‘kare ma d’akin kallo, d’aki ne had’ad’d’e da royal bed aciki, ga kujeru guda uku a ta gefe, da d’an ‘karamin carpet had’e da centre table, d’akin dai ya tsaru gaskiya. Takalmi flat shoe ta saka ta sauko ‘kasa, anan ta tarar dashi zaune a parlour yana kallon tv yana shan tea, tun da ta shigo yake binta da kallo kaman maye, zama tayi a kan kujera tace “Ina kwana ya Sultee?”, murmushi ya mata sannan yamata alamun tazo, cike da fargaba ta nufi kujerar da yake zaune, ajiye cup din yayi sai ya jawota ta fad’o jikinshi, acikin kunnenta ya rad’a mata “Haka ake gaisuwar?”, gyara zama tayi tana sunkuyar da kai tace “Eh mana”, kallonta yayi yaga ta mishi kyau, a hankali yace “Ni banason irin wannan gaskiya”, d’agowa tayi tace “irin wanne kakeso?”, murmushi ya mata ya ‘kura mata ido, yayi kissing nata na minti biyu sai ya saketa yace “Irin wannan”, cike da kunya ta fara ‘ko’karin tashi daga jikinshi, jawota ya ‘kara yi yace “Sarkin kunya, ina zakije?”, kanta a sunkuye tace “Breakfast zan d’aura mana”, tashi yayi cikin sauri yace “Sorry babyna, na saya ai tun dazu but kina bacci saisa ban tasheki ba”, wasa da yatsun hannunta tafara tana mamaki wai yau ya Sultee ne ke mata abubuwan nan, har yana kiranta “babyna”, dawowarshi ne ya katse mata tunaninta.
Feeding nata yayi, tun tana tutturjewa har ta d’an saki jiki ya bata tayi nak, kwanto da ita yayi jikinsa suna kallon tv, Nafisa duk sai taji ta a takure, ahankali ta fara zamewa, ri’kota yayi yace “Yadai?”, a hankali tace “Girki zan mana”, girgiza kai yayi yace “Noo jiya fah muka iso, ki huta tukunna sai bayan 2days sai ki fara mana girkin, zan dinga siyo mana a restaurant”, ba don taso ba tace “Toh”, chan kuma kamar an mitsileta ta tashi tace “Ya Sultee ayyah kiramin su daddy muyi magana”, Sultee ya ‘kara janyota ya d’aurata akan cinyarshi yace “Okay” sannan ya ciro wayarshi daga aljihu. Kira d’aya biyu daddy ya d’aga, gaishe shi yayi tukunna yaba ma Nafisa, cike da d’oki ta kar’ba suka gaisa, sun d’anyi hira sannan sukayi sallama, saida tasa ya kira mata su Amira, Ammi, Mummy, Hauwa, Ukasha, sannan ta ‘kyaleshi. Sunacin abincin rana sai Saleem ya kirashi, sun gaisa normal, Nafisa ta fara jijjigashi “Ya Sultee zanyi magana dashi, ka bani”, Saleem daga d’ayan ‘bangaren yaji muryar Nafisa tana magiya kuma yasan ya Sultee ba bata zaiyi ba, dariya yayi yace “Ya Sultee bata don Allah muyi magana”, sawa a speaker yayi sannan ya mi’ka mata wayar yace “minti d’aya”, ta fara ‘ko’karin mi’kewa don ta haura sama amma ya Sultee ya dam’ke mata hannu, kallonshi tayi taga ya wani had’e rai, tuni tasha jinin jikinta, komawa tayi ta zauna suka shiga gaisawa da Saleem, basu wani dad’e ba ta kashe wayar. Ya Sultee ya watsa mata wani kallo ya fizge wayarshi yace “Bakida hankali ko?, na fasa saya miki wayar ma don naga har yanzu kanki yana mugun rawa”, idonta ya ciko da hawaye tace “Don Allah kayi ha’kuri, bazan sake ba”, ta dinga bashi ha’kuri da ‘kyar dai ya ha’kura.
Da daddare tun suna gama dinner ta gudu d’aki don yinin ranar gaba d’aya a jikinshi tayi, ko motsi baya barinta tayi, sai wani shishshige mata yakeyi, ita yanzu tsoronshi ma takeji yanda yake nuna mata d’okinshi a fili. Around 9 ta fito daga wanka daga ita sai towel tana tsaye a gaban mirror tana goge kanta da ta wanke, ji tayi an rungumeta daga baya, zuciyarta ya buga dumm!!, jiki ba ‘kwari tace “Ya Sultee bari na saka kaya please”, girgiza kanshi yayi yace “umm umm” sannan ya juyota tana fuskantarshi, vest ne fari ‘kal ajikinshi sai three quarter, ahankali ya fara shafata, gaba d’aya yana neman dagula mata lissafi, tanaso ta tureshi amma ta kasa, kwance towel din yayi ya yar a ‘kasa, gaba d’ayansu suka zube akan gado, nan ya fara mata wasu abubuwa masu wuyan ganewa, in banda hawaye ba abinda takeyi, saida yayi iya son ranshi sannan ya ‘kyaleta ya kwanta a gefe yana maida numfashi, da sauri Nafisa taja bargo ta rufe jikinta tanata hawaye, bayan Sultee yaji ya d’an dawo daidai ne ya dauketa chak sai toilet, tare sukayi wanka suka fito, Nafisa ta kasa had’a ido dashi don wani kunyar shi takeji sosai, shikuwa gogan sai murmushi yakeyi yana ‘kara mannata a jikinshi. Daren ranar a d’akinta ya kwana, yana rungume da ita kaman za a ‘kwace mishi ita. Washegari haka sukayi sallah sannan yace ta tashi suyi nafila, sunyi sun idar sannan ya mata tambayoyi ta amsa, suka yi addu’o’insu sannan suka koma bacci. Da safe ta tashi a hankali da niyar shiga toilet tayi wanka, tana mi’kewa yana farkawa, cikin bacci yace “Ina zakije?”, kanta a ‘kasa tace “Wanka zanyi”, mi’kewa shima yayi yace “muje muyi”, ja da baya tayi tana rufe fuska tace “Allah ya Sultee ni bazan iya ba”, murmushi yayi ya kamo hannunta yace “Muje, zaki saba”, tare sukayi wankan bayan ya gama wasanninshi, mai ma shi ya shafa mata sannan ya shafa ma kanshi, da zatasa kaya ya zauna ya ‘kura mata ido, cike da kunya tace “Ya Sultee kaje kasa kaya mana, nima barinsa sai nazo na sameka a parlour’n ‘kasa”, murmushi yayi yace “Kunyar bai fita ba ko?, barinzo na ‘karasar dashi”, ahankali ya soma takowa zuwa inda take, damke towel d’in tayi tace “Yi ha’kuri, zansa”, dariya yayi ya koma kan kujera ya zauna, riga da skirt ta saka, sun kar’beta sosai. Ya Sultee ya tashi ya ja hannunta yace “Zo ki rakani nasa kaya na sai mu fita”, binshi kawai takeyi har suka isa d’akinshi, zama tayi a bakin gadonshi shima sai yazo ya zauna, a sanyaye tace “Ka fasa sa kayan ne?”, girgiza kai yayi kaman ‘karamin yaro yace “Ki fitar min da kayan da zansa mana toh”, cike da mamakin abubuwan da yake tsiro mata take kallonshi, chan sai tace “Da kam wa yake fitarma?”, murmushi yayi yace “Okay tunda baza ki iya wahala na ba, zanje na ‘karo aure kawai na samo mai sona”, ji tayi maganar ya daki zuciyarta, ta rasa gane meke damunta, mi’kewa tayi ta bud’e wardrobe nashi ta fitar mishi da black jeans da white shirt, sai vest da boxers da belt. Wajen sa kaya ma yace shi ina!! bai iya ba saidai ta sa mishi, ta juya bayanta tace “Toh amma kasa boxers din in yaso sai nasa maka sauran”, dariya yayi sannan ya saka ya matso daidai bayanta yace “Okay juyo ki sa sauran”, rufe ido tayi ta saka mishi vest da wando, ta samishi riga tana buttoning sai ya kama hannunta, d’ago kanta tayi tana kallonshi, cike da shagwa’ba tace “Ka bari na ‘karasa sa maka mana”, kamota yayi ya matseta a jikinshi yana sunsunar ta yace “I love you”, kalmar tazo mata a bazata don bata ta’ba tsammanin ya Sultee zai furta mata ba, jan hannunshi tayi tace “nidai muje muci abinci, inajin yunwa”, breakfast sukayi suna hira abunsu. Bayan la’asar ya d’auketa suka fita sha’katawa sannan ya kaita shopping duk da ba wani kayaki take bu’kata ba amma haka ya dinga jida mata kaya kaman ba da kud’i zai siye su ba, ya bata waya irin nashi i-phone 6+.
Haka zamansu ya kasance, kullum tare suke yini da yake hutunshi bai ‘kare ba itama kuma saura kwanaki ya ‘kare, ya saba mata da jikinshi sosai, ya koya mata yanda zata soshi ba tare da saninta ba, ko wani dare sai yayi wasanshi da ita amma bai ta’ba mai gaba d’ayan ba don yasha alwashin sai in Nafisa ta furta mishi tana sonshi sannan zai yarda ya ta’bata. Yau ya kama monday, tanata sauri don kar tayi lattin gashi Sultee sai ‘bata mata lokaci yakeyi, komai ita take mishi kaman wani jinjiri wai sai yace shi bai iya ba, saka kaya kam yazama aikinta don har ta saba yanzu tabar kunyarshi, sai surutu take mishi don Allah yayi sauri ya sauketa a school. Cikin hanzari yafito ya rungumota jikinsa suka shiga motar, yana driving yana murza hannunta guda d’aya, sunata hira suna dariya, in ka ga Sultee baza kace shi bane, yayi kyau, yayi jiki, ya ‘kara haske, Nafisa kuma ta ‘kara cika tayi fresh, kana ganinsu kasan suna matu’kar kula da junansu. Yana parking yafito ya bud’e mata ‘kofar motar ta fito, light kiss ya mata sai yace “Take care of yourself for me, zan dawo anjuma, bari naje na duba abu a office tunda hutuna ya kusa ‘karewa”, murmushi ta mishi tace “Okay, bye”, yana tsaye yana kallonta har ta shiga hall din sannan ya koma motar ya tayar ya bar wajen. 10 mins to zata gama lectures d’in ya Sultee ya iso jiran Nafisa, wata yarinya da gani itama ‘yar 9ja ce ta iso inda yake jingine da motar, gaishe shi tayi ya amsa ba yabo ba fallasa sannan ya cigaba da danne dannenshi a waya, chan sai ta sake cewa “Umm, wa kake jira ne?”, cike da ‘kosawa yace “Mata na”, nan ta fara mishi zuba “Wow, she is so lucky, ta samu handsome guy irinka, how i wish nima zan samu irin haka”, maganar caraf a kunnen Nafisa da ta nufoshi. Tsayawa tayi cak tana kallonshi sai murmushi yakeyi, ita a tsammaninta da budurwar yakeyi, batasan da waya yake murmushi ba, tsaki taja ta juya zata bar wajen, juyowa yayi ya ga ita ne, da sauri ya sha gabanta yace “Babyna, waya ‘bata miki rai haka?”, kallon ka ma raina min wayo ta mishi sannan tace “Ka tafi wajen budurwar ka mana, ba kuna hira bane?”, cikin rashin fahimta yace “Budurwa na kuma?, a ina?”, girgiza kai tayi tace “Waccan wanda kake ma murmushi”, kallon wajen yayi yaga yarinyar d’azun nan ne kuma har yanzu tana tsaye tana kallonsu, tsaki yaja yace “wallahi bansanta ba, yanzu naganta nima a wajen, batun murmushi kuma ina chattin da ahmed ne yake gayamin ankusa sa date nashi da Amira”, ajiyar zuciya ta sauke tace “Allah yasa dai ba budurwar ka bace”, bayaso ya tsaya cacan baki da ita sai kawai ya jawo hannunta ta fad’o a jikinshi, kissin nata yashiga yi kaman mahaukaci, bata hanashi ba don ko ba komai tasan zata ‘kular da yarinyar chan, wani dogon tsaki sukaji anja, still Sultee bai bar abinda yakeyi ba saida ya lura ta bar wajen, murmushi ya ma Nafisa yace “Na kashe maganar, inda budurwa na ne ai bazanyi kissing naki a gabanta ba”, murmushi ta mishi tace “Yawuce”, hannunta ya kama suka shiga motar. Har suka isa gida zuciyar Nafisa bai bar zugin kishi ba, Sultee ya lura da haka, duk sai yaji ba dad’i amma a zuciyarshi ya gode ma Allah tunda dai tana kishinshi kenan tana sonshi.
Sultee ya koma aikinshi, komai yana tafiyar musu normal, ko wani yamma sai sun fita yawo, Ahmed da Amira kuwa har ansa date nan da 5 months don tuni Amira ta gayamusu cewa ta samu magani kuma ta warke, ta bar sirrin ‘karyar da tayi tsakaninta da Sultee. Yau ya kama su Nafisa sun samu hutu na sati d’aya, ta dawo gida sai dad’i takeji zata huta, da daddare Sultee yashigo d’akinta yafara mata yanda yasaba amma na yau ya bambanta don har yana sauka ‘kasa, ganin hakan yasa taji tsoro sosai, iya ‘karfinta ta tureshi, ya kwanta yana numfashi sama-sama har bacci ya d’aukeshi. Washegari ya tashi da zazza’bi sosai, jikinshi har rawa yakeyi, Nafisa taji tausayinshi sosai, sai kuka takeyi tana mishi sannu, a ranar ne ta tabbatar ma kanta cewa lallai soyayyar Sultee ya mata mugun kamu, yinin ranar tayishi a wargaje don Sultee ba lafiya, ji tayi inama ciwon zai barshi ya dawo kanta, yayi kwana biyu sannan ya d’an samu sau’ki don ba ‘karamin kulawa Nafisa ke bashi ba. Ranar da ya warke Sultee bai nuna mata komai ba, suna hira ya rungumeta yace “I love you babyna amma ke bakisona ko?, kiyi ha’kuri ki soni, bazan ta’ba zaluntarki ba, i promise you”, idonta cike da hawaye ta rungumeshi itama tace “I love you too ya Sultee, wallahi ina sonka, banyi realizing bane saida ka kwanta zazza’bin nan, i’m so sorry”, wani farinciki ne ya lullu’beshi wanda bazai misaltu ba. A daren kam dai Sultee ya angonce, duk da ya bita a hankali amma kam tasha wahala, kuka tayishi kamar ba gobe don abun ya had’un mata da yawa; Sultee ya manyanta tunda saura kad’an ya cika 40 gashi tunda yake bai ta’ba kusantar na mace ba sai ayau din kuma akanta gashi su baba Rabi sun d’id’d’irka mata magunguna ba adadi.
Da safe ya gyarata ya dinga sa mata albarka, jin kanshi yakeyi kaman wani sabon mutum, azuciyarshi yace “Aure rahma ne”, yayi ta jinyarta har ta warke suka cigaba da soye wansu. Kullum maganarshi d’aya- “Babyna inason yara, Allah yasa nayi ajiya a cikinki”, ita kuma sai dai tayi murmushi tace mishi “Allah ya kawo ya Sultee”, cikin ikon Allah kuwa ko 3 weeks basuyi da daidai tawa ba ta fara laulayin ciki, gwajin farko likita yace tana da ciki, Sultee yayi sujudul shukr ya dinga kwararo godiya ma Allah, aranar both families saida suka ji batun cikin, Nafisa kam abun ya soma bata kunya har ta dinga mishi complain “Haba ya Sultee yanzu shi ne zaka bi ka bazani a dangi cewa inada ciki?, kai ko kunya baka ji?”, had’e fuska yayi yace “Abun murna ne ai babyna, meh na kunya aciki tunda dai ni ne ubanshi?, lallai har yanzu yarinta yana damunki”, cike da kunyar maganarshi ta kai mishi dukan wasa tace “Ni don Allah kabari, Allah kana sa naji kunya”, dariya yayi ya dinga lallashinta yana gayamata yanda yakeson ta da kuma unborn babynsu. Sabuwar shafin kulawa ya bud’e mata, tare suke aikin gida sannan every evening su fita strolling ta arean anguwansu, kwana biyun su da fara fita har ta saba da neighbours nata su biyu amma ba ‘yan africa bane, da turanci suke hiransu kullum.
Lokacin bikin Amira Nafisa tazo da ‘karamin cikinta mai 3 months and some weeks, bini-bini Sultee zai kirata ya tambayeta ya take da babynshi, mutane har dariya suka soma musu shikam ko a jikinshi. Anyi biki an watse, amarya a Manchester zata zauna da yake an ma Ahmed transfer daga Qatar, saidai mu musu fatan zuri’a d’ayyiba.
Bayan biki da sati Sultee da Nafisa suka je Hamaz don Yabi ta damu tanaso taga Nafisa da jikanta da ke ciki, gaskiya Nafisa tayi sa’ar dangin miji don ba ‘karamin tarairaya suke nuna mata ba, Yabi tana matu’kar son cikin. Sunyi sati biyu sannan suka wuce, yana matu’kar kula da ita wane ‘kwai (Ya Allah kabamu masu sonmu tsakani da Allah), kullum baba Rabi, Amira, Ammi, mummy, Yabi duk sai sun kirata su tambayi lafiyarta, ita har tana mamakin su ganin yanda suka ‘kwallafa rai akan cikin nidai nace ba abin mamaki bane in akayi la’akari da shekarun Sultan don kuwa kowanne iyaye sunason ganin jikansu gashi yanzu sun samu ai dole suyi murna sosai. Cikinta ya cika wata tara suka dawo gida don haihuwa, Yabi taso suzo Hamaz amma Abba yace mata tayi ha’kuri tunda dai itama Nafisa za tafi so ta haihu a gidansu kuma anan ba zata sake sosai ba tunda gidan surukai ne, ba don taso ba haka ta ha’kura. Kwana uku da zuwarsu Nigeria cikin ikon Allah ta haifo ‘ya mace kamanninta sak Sultee, murna a wajenshi bazai fad’u ba, washe gari Yabi ta iso kallon jikanta don ta kasa ha’kuri, rungumeta tayi tana tuna lokacin da ta haifi Sultan don yarinyar tafi kama da babanta akan mamanta, baba Rabi ita tayi ungo zoma. Ana jibi suna Amira da Ahmed ma suka iso itama da d’an ‘karamin cikinta, tayi kyau abunta, da ta d’auki babyn har hawaye tayi a zuciyarta tace “Allah sarki, ashe rabon babyn nan ne yasa muka rabu da Sultan”, ranar suna yarinya taci sunan Amira don yace Amira ta cancanci fiye da haka daga wajenshi tunda ita ta sadashi da farin cikinshi, dama Amira tayi shopping na kayan suna akwati biyu, ai tuni tace tunda an mata takwara dole ta ‘kara kaya, sabon shopping ta shiga tayi ma little Amira har akwati biyar, baby ta tashi da akwati bakwai daga wajen takwararta, Sultee kam kaya kaman hauka yayi ma ‘yarshi da Gimbiya, bikin suna sai sam barka don naira yayi kuka, yarinya tayi farin jini. A daren ranar neh Amira ta gayama Nafisa cewa tasan Sultee yana sonta tun bayan aurensu da diary da tagani da dai sauransu har ‘karyar da ta shirya don su daddy su yarda ya saketa ba tare da sunga laifinshi ko nata ba, Nafisa mamaki ‘karara a fuskarta, ta ‘kara tabbatar da lallai Amira mai sonta ne na gaskiya wanda azamanin yanzun nan da ‘kyar asamu irinta,  godiya bila adadin tayi ma Amira saka makon sadau’karwar da ta mata ta kuma yi al’kawarin bazata ta’ba nuna ma Sultee tasan maganar ba.
Ranar da tayi arba’in akayi auren Saleem da wata ‘yar katsina mai suna Amrah, kowa sai yaba hankalinta yakeyi don yarinyar akwai nitsuwa. Bayan bikin ne suka koma ita da Sultee ta cigaba da zuwa school suna kula da Noor.
Bayan 10 years
Ba mu muka waiwaye su ba sai bayan shekaru goma, mun samu Sultee ya ‘kara zama babban mutum, naira ya ‘kara zaunuwa, soyayya tsakaninshi da Gimbiya kuwa kamar yau suka soma, ta gama makaranta amma ya hanata aiki wai yafiso ta dinga kula dashi da yaransu. Yanzu ‘ya’yansu bakwai, Amira wacce ake kira Noor, mai sunan Yabi wato Hafsat amma ana kiranta Mami, Ibrahim takwarar Daddy amma suna kiranshi Anas, Rabiya wacce suka yi ma baba Rabi takwara wacce suke kira da Futha, twins mata Fatima da Maryam takwarar Ammi da mummy ana kiransu Ilham da Ummitah, sai auta mai sunan Abba wato Mu’awiyah ana kiranshi Haneef. Yara kyawawa dasu sai Allah ya raya ya sa su girma akan turban addinin Musulunci. Anan muka ji labarin Amira yaranta hudu: Usman takwarar baban Ahmed suna kiranshi Zunnurayn, Abdullahi, Sultan ‘karami wanda ake kira Boy sai auta Fawziyyah ana kiranta Zeebly. Gidan Saleem da Amrah kuwa yaransu biyar: Nafisa ‘karama ana kiranta Feesha, Sabir, Sadiya, Abbakar Sadiq sai auta Aisha. Family ya ‘kara girma gashi kansu a had’e yake, every december gaba d’aya ake yin family re-union gwanin ban sha’awa.
Ya Allah ka bamu zuri’a d’ayyiba mai albarka(Ameeeeen).
Anan muka kawo ‘karshen littafin nan mai suna Gimbiya Nafeesah, duk kuran kuran da ke ciki Allah ya yafe mana.
Gaisuwa zuwa ga: Aisha Naany(Allah ya saukeki lafiya), Sadydy gulgul, Shukurah, Amirah Maisikeli na Ahmed, Amrah Auwal Mashi, Bahiratu my crazy sis, Milly Balalau, Anty Muma, Hajju, Zainab Sifawa, Kdeey and duk sauran ‘yan Novels Novella da ban ambaci sunayenku ba, Allah ya bar zumunci.
Godiya da jinjina zuwaga Fawziyyah maman Ilham, nagode ma Allah da yabani sister kamar ki, thank u for all the love and support, Jamila Moh Ali bansan ya zan gode miki ba, Allah ya saka da alkhairi, Khadijah body ke ta dabance.
Excellent writers, Mu farka mata 1 & 2, House of novella na kdeey, Yau uwan juna na sisi axland, Zauren karatu na Sis Bena, M.Jabo munbarin hausa novels na Jabo our honourable admin, Be a lady with fashion na Futha, Sahaf’s Novels, Er lele hausa novel group, Maman Aleesha novels, Maman Haneep novels, matan kwarai na Serdeeyer, Hausa novels, Rookie Sadau novels, da ma duk sauran da ban ambata ba we luv you all da soyayyar da kuka nuna ma littafin nan.
Called/WhatsApp @Author @07062678869


0 Please Share a Your Opinion.:

Post a Comment