donforum


HOMEHome
musicMusic
videosVideos
gistsKanny
👉 LATEST DAILY UPDATES 👈

Saturday, May 26, 2018

ABIN DA YASA MUHAMMAD SALAH YA GAGARI TURAWA

Mo Salah:  Abin da ya sa Balaraben Masar ya gagari Turawa? 

Mo Salah
A yayin da 'yan wasa ke murna kan nasarar da suka samu da ci 4-0 kan ENPPI, sai kocinsu Said Al Shesheni ya fahimci cewa akwai daya daga cikin tawagar  
Al-Mokawloon da ya nuna bai ji dadi sosai ba bayan wasan da aka yi a birnin Alkahira.
A zahirin gaskiya ma sai sharara kuka yake yi, damuwarsa shi ne babu sunan shi daga cikin wadanda suka ci kwallayen. Saboda yana buga lamba uku, zai yi wahala ya taka muhimmiyar rawa kamar yadda yake so.
Ya fito ne daga Nagrig, wani kauye da ke da nisan kilomita 130 da Al Kahira babban birnin Masar.
Dan wasan yakan shafe sa'o'i tara a rana yana kai-komo, wani lokaci yana hawan mota 10 kafin ya isa wurin atisaye.
Dan wasan ya ja hankalin kocinsa Al Shasheni inda ya ba shi dama ya mayar da shi dan wasan gaba.
Dan wasan da ake magana ba kowa ba ne illa Mohamed Salah, wanda tun a lokacin tauraronsa ke haskawa.
 SANNAN M.SALAH YA BUDE SABON FILIN BALL.

Mo Salah yana yaro
Wannan labarin zai taimaka ya amsa tambayoyi da dama da ke zukatan masoya kwallon kafa a fadin duniya.
Shin ta yaya aka yi Mo Salah dan wasan da a baya ya fuskanci kalubale a manyan lig lig na Turai, amma yanzu ba zato ba tsammani ya zama dodon raga da har ake kwatanta shi da zaratan 'yan wasa irinsu Lionel Messi da Cristiano Ronaldo?
Wani lokaci, yana taimaka wa idan dan wasa ya samu kan shi a inda ya dace da kuma lokacin da ya dace, ko dai tun a makarantar kwallon kafa ta Masar ko kuma a wasu manyan 'yan wasa na gasar Firimiya.
Lokacin da Liverpool ta sanar da karbo Salah daga kulub din Roma na Italiya a bara, wasu da dama na ganin kudin da aka karbo dan wasan fam miliyan 55.7 sun yi yawa ga dan wasan da ya kasa nuna kansa a Ingila lokacin yana Chelsea a 2015.
Wani abu muhimmi da ya kamata a sani shi ne, duk da cewa Masar ba ta yi fice ba a duniya, amma uwa ce a Afirka domin ta lashe kofin nahiyar sau bakwai.
Sau biyu kawai Masar ta buga gasar cin kofin duniya a (1934 da 1990) da kuma yanzu zamanin Salah, inda ake ganin za su mamaye kanun labarai musamman mai tsaron raga Essam El-Hadary da zai kasance dan wasa mafi tsufa da ya buga a gasar da Masar za ta buga a Rasha.
Salah da Klopp

 Created And Designed By @Aspro


0 Please Share a Your Opinion.:

Post a Comment